8 Yuni 2025 - 21:33
Source: ABNA24
Bidiyon Yadda Aka Buɗe Kamfanin Labaran ÀBNA A Nahiyar Afirka Ghana

Bidiyon Yadda Aka Buɗe Kamfanin Labaran ÀBNA A Nahiyar Afirka Ghana

An Bude Ofishin Yada Labaran ABNA A Ghana domin yaɗa labaran mabiya mazhabar Ahlulbaiti AS da yaɗa koyawar ingantaccen musulunci da koyarwar Ahlulbaiti AS / Kamfanin Labaran ABNA ya kasance Muryar mabiya Ahlul Baiti (AS) a Afirka gaba ɗaya da Yammacin Afirka dama duniya gaba ɗaya domin isar da ingantattun labarai daga madogarar ta ainahi bisa nakaltowa daga majiyoyi gida da waɗanda suka tabbatar da labaran bayan tacewa da gyarawa.

An buɗe wannan sashen ne bisa jagoranci shugaban majalisar Ahlulbaiti AS ta duniya Ayatullah Ramezani da shugaban mai gudanarwa na dukkan kamfanin labaran Sayyid Hasan Sadra'i Arif a cikin tafiyar da sukai zuwa wannan nahiya mai albarka don isar da sakon addinin musulunci da kulla dangantakar alaƙar kut da kut da sauran al'ummar musulmin wannan nahiya.

Your Comment

You are replying to: .
captcha